Tafarfara

Tafarfara Shafi ne dake maida hankali a fagen; Ilmantarwa da Nishadantarwa cikin harshen Hausa.

Mutanen Kogi ta Tsakiya sun fara aikin yin kiranye ga dakatacciyar mai wakiltar su, Sanata Natasha Akpota
20/03/2025

Mutanen Kogi ta Tsakiya sun fara aikin yin kiranye ga dakatacciyar mai wakiltar su, Sanata Natasha Akpota

20/03/2025

DA DUMI DUMINTA: Majalisar Wakilai karkashin jagoranchin Hon. Tajuddeen Abbas ta aminci da kudurin Tinubu na saka Dokar Tabaci, tsige Gomna da Majalisar Dokoki na jihar Rivers!

Ya kamata gomnatin Tinubu tadawo da zababbun shugabannin jihar Rivers, El-RufaiBayanin ya fito ne daga wata sanarwa da y...
20/03/2025

Ya kamata gomnatin Tinubu tadawo da zababbun shugabannin jihar Rivers, El-Rufai
Bayanin ya fito ne daga wata sanarwa da ya fitar a shafukansa na sada zumunta inda yake tabbatar da cewa hakan ya sabawa dokokin Najeriya dana Damokradiya.

Yake cewa "Lallai batun matsalar tsaro da shugaban ya fada maganar ta cancanci a bata sosai don kiya kaddarorin gonmnati, wannan shine abunda muke goyon baya. Kuma daacewa yayi Dokar Tabaci a sanya ta ne domin bawa jami'an tsaro cikakkiyar dama da ishasshen kayan aiki don magance matsalar. Amma fadada lamarin har ya kai ga kwance gine-genen dimokradiya hawan kawara ce ga tsarin dimokradiya da dokoki. A 2006 Kotun Allah Ya Isa dangane da danbarwar Gomna Joshua Dariye da Ministan Sharia, ta fayyace cewa tsige zababbun shugabani ba lamari ne da doka ta amince dashi ba." inji El-Rufain.

EL-Rufai ya tunawa shugaba Tunibu yadda ya nuna rashin goyon bayansa baro-baro a lokacin shugaba Jonathan da yayi kokarin saka Dokar Tabaci a yankin Arewa maso gabas.

Yace, "Sanata Tinubu ya fito karara ya bayyana rashin goyon bayanshi dangane da matakin da Jonathan zai na sanya dokar ta baci a yankin Arewa maso gabas, doka ya zamo lokacin matakin kai ga cewa za'a dakatar da zababbun shugabannin ko wasu ma'aikatu ba."

Inda ya kara da cewa, "Mu guji yin shiru alokacin da abun da ya faru tsohon Yankin Yamma 1962 yana faruwa a gaban idon mu. Ina kira duk yan kishi da masu fade aji da mu hadu wajen kira da kawo karshen karan tsayen da akewa Tundin Tsarin Mulki da da fyaden da akewa Dokoki."

BABBAR MAGANA: Shugaba Tinubu yasa Dokan Tabaci a jihar Rivers, Ya tsige Gomna Sim tare da rushe Majalisar JiharShugaban...
20/03/2025

BABBAR MAGANA: Shugaba Tinubu yasa Dokan Tabaci a jihar Rivers, Ya tsige Gomna Sim tare da rushe Majalisar Jihar

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers, ya tsige gomna Siminalayi Fubara da mataimakiyansa Mrs. Ngozi Odu ya kuma nada Vice Admiral Ebokette Ibas (ritaya)ya rige jihar na tswon wata shidan wucin gadi kafin yaga wani mataki zai dauka a gaba.

Sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban Kasar a yayin da yake zayyano bayani kai tsaya ga zuwa mutanan Najeriya dangane da halin da jiyar take ciki na ruciki tsakanin gomnan da wasu bangarori na siyasa na tsawon lokaci, duk kokari da shi yayi da kuma wasu manya jihar dama Najeriya s**a amma bai haifar da da mai ido ba.

"Ni da kai na nayi kokarin shisshiga tsakani don sulhunta lamari amma duka bangarori s**ai watsi da hobbasa ta". "Kuma Kotun Allah Ya isa yanke hukunci akan hadadden daukara 8 da aka shiga, inda ta tabbar cewa gomnati ba zata taba tabbatuwa ba sai da kinshikanta guda 3." Inshi shugaba Bola.

DA DUMI DUMI: Yan Majalisan Wakilai na Tarayya 2 sun canza sheka daga PDP zuwa APC.Shugaban Majalisar Hon. Tajuddeen Abb...
18/03/2025

DA DUMI DUMI: Yan Majalisan Wakilai na Tarayya 2 sun canza sheka daga PDP zuwa APC.

Shugaban Majalisar Hon. Tajuddeen Abbas ya bayyana hakan a lokacin da yake karanta takardun sanarwar ficewar tasu yau a Talata 18 ga Maris 2025 a mazaunin Majalisar dake Abuja.

1. Hon. Adamu Tanko, mai wakiltan Gurara/Suleja/Tafa ya fide daga PDP zuwa APC.

2. Hon. Husain Mohammed Jalo, Dan-Majalisa mai wakiltan karamar hukumar Igabi take dake Kaduna, ya fice gada PDP zuwa APC.

Majalisar Wakilai Najeriya karshin jagorancin Hon. Tajuddeen Abbas PHD, ta baiwa Gomnatin Tarayya Naira Miliyan 705 a ma...
18/03/2025

Majalisar Wakilai Najeriya karshin jagorancin Hon. Tajuddeen Abbas PHD, ta baiwa Gomnatin Tarayya Naira Miliyan 705 a matsayin gudummuwar ayyukan jin-kai da gomnatin ke yi.

SHUGABA TUNIBU YA AMINCE DA NADIN REBREN MATTHEW KUKAH A MATSAYIN MATAIMAKIN CHENSELO NA SABUWAR JAM'IYAR FASAHA TA TARA...
18/03/2025

SHUGABA TUNIBU YA AMINCE DA NADIN REBREN MATTHEW KUKAH A MATSAYIN MATAIMAKIN CHENSELO NA SABUWAR JAM'IYAR FASAHA TA TARAYYA NA KACIYA DAKE KUDANCIN NAJERIYA.

Shugaba Tinubu Ya amince da nadin Rebren Matthew Kukah (Jagoran Roman Katolika na Sokkoto, Mamba a Kungiyar Ciristoci na Cikagaban Dan Adam wanda Fafaroma ya kafa) a matsayin mataimakin chanselo na sabowar jam'iyar koyan fasaha ta Kachiya dake kudsncin Kaduna.

Sanarwar ta fito ne daga bakin maigrima maitakin shugaban Kasa, Kashim Shettima a yayin da yake yabawa salon jagorancin Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Hon. Tajuddeen Abbas yayinda s**a amsa gayyatar shugaban kasa zuwa shan ruwan Azumi na 17 a yammacin jiya Litinin, inda yace shugabanci na gari shine wanda ake tafiya tare wani bangare na al'umma. Ya kara da cewa, "Kai dani duk mun san cewa APC ba tayi kokari a baya ba a kudancin Kaduna"

Dan takaran shugabancin Najeriya na jam'iyar LP a kakar siysasa ta 2023, Peter Obi ya taya musulmai shan ruwa a jiharsa ...
18/03/2025

Dan takaran shugabancin Najeriya na jam'iyar LP a kakar siysasa ta 2023, Peter Obi ya taya musulmai shan ruwa a jiharsa ta Anambra.
Tsohon gomnan Anambra ya halarci shan ruwan azumin watan Ramalana a babban birnin Awka da kuma babban Masallacin birnin Onaca a ranar Juma'a da Asabar.

Babban abun da yafi daukar hankalin jama'a shine yadda aka hange shi a wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta tare da kananan yara 3, buyu maza, 1 mace suna tseren lomar shinka dafa duka.
Inda abun ya jawo cece kuce sosai, har wasu suke ganin wannan ba wani abu bane face tsananin dimaucewarsa kan zamowa shugaban Najeriya.
Daidai lokacinda wasu ke cewa basu ga laifinsa ba tunda ai haka halayyan yan siyasa yake wajen ganin sun cimma burinsu ta siyasa ko ta ko wace hanya musamman a Najeriya.

EL-RUFAI YA BUDE SHAFIN TIKTOK, YA SAMI MABIYA KUSAN 400,000 CIKIN KWANAKI 3. Kwatsam aka tsinci bidiyo mai tsawon rabin...
16/03/2025

EL-RUFAI YA BUDE SHAFIN TIKTOK, YA SAMI MABIYA KUSAN 400,000 CIKIN KWANAKI 3.

Kwatsam aka tsinci bidiyo mai tsawon rabin minti na tsohon gomnar jihar Kaduna yana shedawa jama'a cewa sabon shafin kenan a durance kamar haka;

"Sannnku, sunan Nasir El-Rufai, wannan shine shafi na kadai na gaskiya a kafar Tiktok. Ina gayyatar ku don samun bidiyo, tsokaci, da tattaunawa dangane harkokin siyasa, gomnati Najeriya da kuma ayyukan sabuwar jam'iyar mu SDP, lale da shigowa." Inji shi

Da yike kwararren dan gwagwarmaya ne mai tasiri a siyara Najeriya, wanda mutane suke rajin jin albarkacin bakin sa a kullum, shiyasa shafin nasa sami kalubalen kafuwa ba, inda cikin awa 24 bidiyon farko na sanarwar nashi ya sami mabiya sama da 200,000, masu kallo sama a miliyan 1.9, masu shari sama da 21,000, inda bayan kwanaki 3 shafin ya sami karin mabiya sama da 100,000 masu kallon bidiyon kuma sama da miliyan 2.6.

ALAMOMI NA NUNA CEWA AN KADA GANGAR SIYISAR NAJERIYA TA 2027!A kwanakin nan ne dan shugaban kasar Najeriya Seyi Tinibu y...
16/03/2025

ALAMOMI NA NUNA CEWA AN KADA GANGAR SIYISAR NAJERIYA TA 2027!

A kwanakin nan ne dan shugaban kasar Najeriya Seyi Tinibu ya fara wata rangadi zuwa jahohin kasar, inda aga gansa yana ziyartar masarautu, malumma 'yan siyasa da kuma shirya taron shan ruwa a kewaye da 'ya'yan gomnoni da masu ruwa da tsaki a gomnatocin ta tarayya dana jihohi da kuma shugannin matasa da kuma mawaka don rakiya, qarfafawa da nuna gogon ga abunda yazo ashi, ana masu wakoki da bambadanci shi da ubanshi, ya kuma raba masu abinchi!

A wani bangaren kuma ana ta rade-radin wasu jigajigan siyasar jihohi da masu ruwa da tsaki a jam'iya mai mulki da na adawa kamar tsoffin gomnoni, ministoci da komishinoni da ma suna ta shirye shiryen tsallen sauya sheka daga jam'iyoyinsu zuwa wasu. Wasu don komawa mai mulki wasu kuma don barin mai mulki. Kowa da korafinsa na rashin samun biyan bukatunsa a gomnatance, jam'iyance ko a Najeriyance ga wadanda suke ikrarin suna siyasar don cigaban kasa da walwalar don kasa kenan!

Abunda yafi yamutsa hazo a kwanakin nan a kafafren sada zumunta shine fircewar fitaccen dan gwagwarmayar siyasa a Najeriya, daya daga cikin 'yan gaba a kafa APC, kuma tsohon gomnar jihar Kaduna wato mallam Nasir El-Rufai daga jama'iyar APCn zuwa SDP.
Wanda tun kafin ficewar tasa yata nuna rashin gamsuwarsa ga yadda APCn take tafi da lamarin jagorancin gomnatin kasar, jihohi da kuma lamarin jam'iyar. Inda yace gaba daya sun sauka daga kan tsarin gudanarwa ta jam'iya wanda shine; tsaro, lafiya ilimi, dakile rashawa, lantarki walwala da sauransu. Wadannan suna daga cikin lamurran da s**a kara saka ruwa tsami tsaninsa da aminansa na gomnatocin tarayya dana jiha, kamar gomnar jihar Kaduna wanda El-Rufain ne yayi uwa yayi makarbiya wajen daurashi a karagar jagorncin jihar bayan kammala wa'adinsa, wanda a kwanakin kuma aka jiyo El-Rufain yana masa Allah Ya isa da tsinuwa bisa amfani da jamian tsaro da gomnar keyi don gallaza masa shi da mutanensa gami da tsare wasu akeyi babu dali a cewarsa.
A yayinda a wasu gurare aka jiyo yana kiran amininsa kuma surukinsa, mai baiwa shugaba Tinubu shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribado, ba mutum bane, mara amana, makaryachi da dai sauransu.
An kuma kara jiyo shi yana kira ga jigogin adawar siyasar Najeriya kamar su: Alh. Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amechi da sauransu da su shiga SDP don su hada karfi da karfe don fatattakar gonmatin APCn! Ko hakan mai yiwuwa ne?

Wata Kila ka na ta kokarin maimata zuwa dakin Kaaba don neman kusanci ga Allah, ko don biyan bukatun ka ko Dan ado da Al...
05/02/2024

Wata Kila ka na ta kokarin maimata zuwa dakin Kaaba don neman kusanci ga Allah, ko don biyan bukatun ka ko Dan ado da Alfahari,to Amma ga wasu dakunan kaabah kusa da Kai na marayu da na marasa karfi Wanda ake so Kai dawafi wurin taimakon su kafin Kai tunanin zuwa kaaba.
الكعبة أمام بيت كل منا
فقط علينا ان نحسن الطواف
kudin da za ka kashe zuwa kaabah Mai nisa zai iya sanadin rayuwar mutum dari biyar acikin shekara.

Wanda rahama ta sauka a zuciyar sa kuma ya gano kusanci da Allah acikin taimakon bayin sa, to hakika ya shiga cikin masana Allah.

Kai dawafi gidan talakawa da marayu yafi dawafin Alfahari Kuma yafi kusanci ga Allah.

28/01/2022

Assalamu alaikum, barkanmu da wannan rana mai albarka, da faran kowa yatashi lafiya, Allah yabamu albarkan da yake cikin wannan rana, juma'a mubarak

Address

Khartoum

Telephone

+249929846833

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tafarfara posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share