Usmaniya Agrovet Investment Rahama

Usmaniya Agrovet Investment Rahama I

01/05/2025

DA ƊUMI ƊUMI: Al'ummar Musulmai Sun Nuna farin cikinsu Bisa jin Wannan daddaɗan Labarin, Za'a Rubuta Sunan Ganduje A Cikin Kundin Sunayen Mutanen Da S**a Ba Wa Musulunci Gagarumar Gudunmawa A Ƙarni Na 21 A Cikin Kundin Tarihin Musulunci

Ƙasar Saudiyya ta duƙufa wajen tsara biki na musamman domin karrama mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a dalilin namijin ƙoƙarinsa wajen musuluntar da maguzawa sama da mutum dubu goma batare da zubar da jini ba.

A cewar mahukuntar ƙasar, abin da Gandujen ya yi wata babbar gudunmawa ce ga addinin musulunci wacce babu wani ɗan siyasa da ya taɓa ba da irinta a Afrika ta yamma gaba ɗaya a wannan ƙarni na 21 tayadda hakan ke nuni da yadda gwamnan ya cancanci yabo.

Ƙasar ta Saudiyya ta kuma ƙara da cewa a dalilin wannan ƙoƙari da Ganduje ya yi, za ta rubuta sunansa a cikin kundin tarihinta wanda ta samar domin rubuta sunayen mutanen da ke ba wa musulunci gudunmawa mai girma a Nahiyar Afrika.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ƙasar ta Saudiyya tayi bah.

Allah ya kara maka karfin gwiwa taimakon addini.

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu Ya Ba Da Tallafin Naira Biliyan 110 Ga Jami’o’i 18A ƙoƙarinsa na magance m...
30/04/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu Ya Ba Da Tallafin Naira Biliyan 110 Ga Jami’o’i 18

A ƙoƙarinsa na magance matsalar fitar ƙwararrun masana kiwon lafiya ƴan Najeriya zuwa ƙasashen waje yin aiki, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a fidda Naira Biliyan 110 a matsayin tallafi ga jami’o’i 18 da aka zaɓa a faɗin ƙasar.

Shirin wata manufa ce ta kyautata ilimin lafiya gami da bunƙasa ingancin jami’o’i su riƙa samar da ƙwararrun masana kiwon lafiya, kamar yadda Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

Kowace jami’a ɗaya za ta samu kuɗaɗen da yawansu ya kai Naira Biliyan 4 da kuma Naira miliyan 750 da aka ware musamman domin gina gidajen kwanan ɗalibai. Za kuma a yi amfani da kuɗaɗen wajen samar da manyan ɗakunan gwaje-gwaje na zamani guda guda 8 waɗanda za a raba su a shiyoyin ƙasar a wani mataki na faɗaɗa shirye-shiryen kiwon lafiya.

Jami’o’in da za su ci gajiyar tallafin sun haɗa da:

1. Jami’ar Nnamdi Azikwe (Nnamdi Azikiwe University)
2. Jami’ar Jihar Bayelsa, (Bayelsa State University)
3. Jami’ar Legas, (University of Lagos)
4. Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (Ahmadu Bello University)
5. Jami’ar Benin (University of Benin)
6. Jami’ar Imo (Imo State University)
7. Jami’ar Ibadan (University of Ibadan)
8. JAmi’ar Kimiyya Ta Ondo (University of Medical Sciences, Ondo)
9. Jami’ar Benue (Benue State University)
10. Jami’ar Ƴar’adu’a (Umaru Musa Yaradua University)
11. Jami’ar Nsukka (University of Nigeria, Nsukka)
12. Jami’ar Kalaba (University of Calabar)
13. Jami’ar Tafawa Ɓalewa (Abubakar Tafawa Balewa University)
14. Jami’ar Jos (University of Jos)
15. Jami’ar Ilorin (University of Ilorin)
16. Jami’ar Jihar Gombe (Gombe State University)
17. Jami’ar Ɗanfodio (Usmanu Danfodio University)
18. Jami’ar Maiduguri (University of Maiduguri).

Tallafin zai kuma yi amfani wajen gudanar da ayyuka a makarantun lafiya ta hanyar gyara ɗakunan ɗaukar darasi, zamanantar da ɗakunan gwaje-gwaje na kimiyya, gami da kyautata harkokin koyo da koyarwa.

Ana kuma sa ran shiri

ABIN A YABA: Malama Hajara Kenan Wacce Ta Gina Katafaren Sabon Masallaci A Unguwar Ndeshi Dake Karamar Hukumar Mokwa A J...
26/04/2025

ABIN A YABA: Malama Hajara Kenan Wacce Ta Gina Katafaren Sabon Masallaci A Unguwar Ndeshi Dake Karamar Hukumar Mokwa A Jihar Neja

Wane fata za ku yi mata?

Mun samu labari mai tushe Presidency ta gindayawa ƴan APC da ba sa son Kwankwaso ya shigo jam'iyyar sharaɗin cewa sai in...
26/04/2025

Mun samu labari mai tushe Presidency ta gindayawa ƴan APC da ba sa son Kwankwaso ya shigo jam'iyyar sharaɗin cewa sai in sun amince 2027 su za su ciyowa kansu zaɓe ba tare da gudunmuwar Gwamnatin tarayya ba, kunga inda Gizo ke saƙar kenan - Hon. Auwal Aranposu

24/04/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta na bayyana cewa shahararren mai fafutukar ƙwatar 'yancin bil-adama, wato Ahmad Isah (Ordinary President), yana buƙatar addu'a ta musamman domin yana cikin sarƙaƙiya.

Allah Ubangiji ya kawo masa ɗauki na gaggawa.

23/04/2025

Wallahi idan kaga Shugaba Tinubu bai dawo ba a zaben 2027 sai dai in mutuwa ya yi, inji ƴar siyasa a jam'iyyar APC Maryam Kofar Mata

Ta bayyana hakan ne ta cikin shirin (Podcast) na Jaridar Dokin Ƙarfe TV.

Ku ziyarci shafinmu na Youtube domin samun cikakkiyar tattaunawar kaitsaye a wannan link ɗin https://youtu.be/2eYqNWKVBXM?si=tEJVhBv6NVLjrVvQ

Menene ra'ayinku?

23/04/2025
KUYI DUK abin da kukeso zamu barku da Allah Amman kar ku taba mana Annabinmu wallahi baza mubari  (is a read line unacce...
23/04/2025

KUYI DUK abin da kukeso zamu barku da Allah Amman kar ku taba mana Annabinmu wallahi baza mubari (is a read line unacceptable ) KU BARMU DA MAZON ALLAH

Address

Rahama Rawun
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Usmaniya Agrovet Investment Rahama posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Usmaniya Agrovet Investment Rahama:

Share