24/05/2026
MACE MUTUM CE!(3)
Ci gaba...
Kamar yadda muka kawo cewa,..
Kallon mace a ba wata tsiya ba kuma bata da wata kima dadadden lamari ne da ya shahara tun kafin zuwan musulunci,akwai al'umar da su ke rayuwa suna sanya mata acikin kayan gado,misali mutum zai iya gadar matan babansa ciki harda mahaifiyarsa idan ya mutu.
Akwai Al'umar da su ka rayu,Idan mazajensu sun mutu saidai a hada su da matansu a bizne su,kuma wannan mace bata da zabi,tana ji tana kallo tana kuka haka za ta kwanta kusa da mataccen mijinta a bizne su,kuma har yanzu akwai irin wannan al'umar suna rayuwa a haka,amma idan ita ce ta mutu shi zai iya sake auren wata.
Bari na dan hakaito mana wata kissa da ta faru wadda Allah Subhanhu wa ta'ala ya kawo ta acikin Alqur'ani.
Ya zo a sira cewa,..Ita Mahaifiyar Sayyada Maryam as ta yi bakance ga Allah cewa..ta na so ya ba ta da namiji da za ta sanya shi mai yin hidma a baitul muqddas,watakil share-share da gyarawa masu ibada takalma idan sun ajiye wanda ta ke kallon wannan a wata sadaukarwa ga ubangiji.
Bayan ta haifi sayyada Maryam sai ta ji a zuciyarta cewa bata samu abinda ta ke bukata ba,domin Mace ta haifa.
Sai ta ke gayawa Allah cewa...Ya Ubangiji ka ga alkawarin da na yi maka da irin burina na samar da wani Da namiji da zai zama mai hidma ga masu ibada,har ka ce ka amsa min,amma yanzu na haihu sai na ga na haifo mace,me hakan ya ke nufi?.
Sai Allah ya ce mata kada ki damu Namiji bai kai mace ba..k**ar muce Allah ya raba rigimar tun anan idan ana da tunani,Allah da kansa yace Namiji bai kai mace ba,amma Allah bai bar abin haka ba saida ya nuna wata aya da har zuwa yau din nan ba wani namiji da ya samu wannan matsayin,ayar kuwa ita ce.
Lokacin da sayyada Maryam as ta kai kololuwa wajen ibada,sai Allah ya ce da ita,...Ya ke Maryam..yanzu za ki iya shiga masallaci ki hada sahu da maza a yi ibada tare da ke ki yi sujuda atsakiyarsu ma'ana ki yi sujuda ki yi ruku'u duk tare da su..Tambaya....shin akwai wani Namiji da Allah ya taba cewa..yanzu ka shiga tsakiyar mata ka yi ibada tare da su ana gogayyar jikin juna?
Wannan yana nuna mana irin karfin ruhin da 'Ya mace ke da shi wanda ya ke kaita ga musharaka da maza ba tare da taraddudin za'a samu matsala a Imaninsu ba.
Wannan yana nuna mana yadda kowace Al'umma take da ilimin cewa,ko Malami ne ake so ya lalace to a hada shi da mace saboda su maza ba su da irin wannan tsarkin ruhin..shi yasa Azzaluman mahukunta da su ka rayu da Imamai as su ma su sun yi kokarin gwada Imamai as ta hanyar hada su waje daya da mace a kurkuku dan aga yadda zata kaya,wanda Allah da ikonsa babu wani Imami da aka yi galaba akansa saboda tsarkinsa,..dalilin kawo wannan shine....ku san kowace Al'umma sun yanke hukuncin ba wani Namiji da zai iya tsallake cudanya da mace ba tare da ya halaka ba,alokaci guda kuma ga macen da Allah ya bata wannan girman.
Ya zo a tarihi kafin zuwan musulunci har zuwan musulunci larabawa idan aka haifa musu mace suna bizneta ko su tafi da ita bayan gari su kasheta su jefar,..idan aka gayawa mutum an haifar masa mace sai ya qwansare fuska fuskarsa ta yi ja saboda an haifo masa tashin hankali....
Wannan fa duk muna so mu nuna yadda maza su ka taso ne tun asali da jin cewa mace ba komai bace,su maza sune halitta mai girma da dara.
YADDA MANZON ALLAH SAWW YA SAUYA TUNANIN AL'UMMA AKAN MACE.
Yana daga cikin abinda ya sauya tunanin al'umma irin yadda manzon Allah saww ya sauya fasalin yadda ake kallon mace.
Kada mu dauka akan Sayyada Fatima as manzon Allah ya fara sauya wa duniya tunani,lallai ya aikata hakan har a abokansa na kiwo yadda ya ke girmama su suna yara,har zuwa sayyada Khadiji da ta zama matarsa,ta yadda ya ke mikewa tsaye idan ya ganta kuma ya ke mata magana da gurmamawa kai wannan falalar saida ta shafi kawayen sayyada Khadija wanda ba tarihin muke so mu kawo gaba daya ba,muna tunawa kawukanmu ne cewa,tuni manzon Allah saww ya yaki wannan tunanin.
Manzon Allah saww ya buga samfur da sayyada Fatima as yadda itama ya ke girmamata,..Ance wani sahabi ya ga manzon Allah saww ya sumbaci wiyan sayyada Fatima as sai ya ke cewa manzon Allah ...Macen ka ke yiwa haka?...Sai mazon Allah saww ya ce masa..shin kai baka aikata haka akan yarka?..sai ya ce Eh..a take manzon Allah ya sauya fuska kuma ya umarce shi da ya rika aikatawa yayansa mata hakan.
WATAKIL YADDA NAMIJI KE KALLON MACE A BA KOMAI BA SHINE YA HADDASA MATSALOLI DA YAWA NA ZAMANRAKEWAR AURE.
Wato idan za mu kawo tarihin Al'umma ne game da yadda su ke kallon mace lallai za ku gazgata cewa,wannan kallon zai iya yiwuwa shine ya sabbaba matsaloli da yawa na zamantakewa.
Za mu ci gaba Insha'Allah
Shareef Muhsan Bachirawa
08034318311
24/05/2026