Kafin Hausa Unity Forum

Kafin Hausa Unity Forum To bring Cooperation coexistence, and development in to our local government community.

13/06/2026
‎Duk wanda ya ga NASSCO ta tura masa wannan saƙon ta layin wayar sa, ya jira zai kaga Credit Alert cikin satin nan ko ne...
11/06/2026

‎Duk wanda ya ga NASSCO ta tura masa wannan saƙon ta layin wayar sa, ya jira zai kaga Credit Alert cikin satin nan ko next week ɗin da za'a shiga. NASSCO tana nufin National Social Safety Nets Coordinating Office. Wani Office ne a ƙarƙashin Federal Government wanda yake bayar da kuɗaɗen tallafi ga gidajen 'yan ƙasa marasa ƙarfi waɗanda bayanan su suke cikin National Social Register (NSR). Tun last daman hukumar NASSCO ta sanar da State Representatives ɗin ta cewa su tura bayanan duk waɗanda s**a tantance saboda su cigaba da bayar da tallafin Renewed Hope kamar yadda s**a bayar a shirin RRR da kuma Conditional Cash Transfer (CCT).

‎A wannan lokacin, hukumar NASSCO ta fito da tsarin buɗewa mutane account ne da bankin UBA saboda suyi gaggawar turawa mutane tallafin 75k ɗin su kai tsaye maimakon ace sai sun fitar da list sannan mutane suna ta turarreniya a kan layi ko a wurin State Verification Officer ɗin su kafin su karɓi tallafin su. A wannan lokacin da zarar ka ga wannan message ɗin mai ɗauke da account number ɗin ka kawai ka jira Credit Alert very soon ka je ka cire kayan ka da kanka nan take. Na ajiye link na Original page ɗin su a comment section koda kana neman ƙarin bayanai. Ku yi sharing saboda mutane su fahimta don kar su goge account ɗin su ɗauka scammers ne. 🙏

07/11/2025

MA SHA ALLAH: Agobe asabat Maigirma Gwamna Malam Umar Namadi shi Zai jagoranci gaddamar da Bada tallafi agurin bikin yaye Wadda aka koya musu sana'o'in hannu Daban-daban anan Cikin Garin Kafin Hausa.

An Bada horonne ga matasa Maza da mata Wadda S**a kammala karatun DEGREE, HND NCE ND, ba su da aikin yi, saboda karfafa musu gwaiwa, da Kuma Kara Nuna musu mahimmancin karatun da s**ayi musan mutanen karkara ba sai sun Jira Gwamanati ta ba su aiki ba,

Taron Zai samu Halarta Mayan mutane Daga ciki
Akwai Dr Habibu M Ubale DG empowerment
Komishinan lafiya
Komishinan mata,
Shugaban Karamar Hukumar Kafin Hausa.
Yakubu AH Ruba SAN
Maigari Usman
Dupety chief of staff
Abdullahi Hudu
Ibrahim Adamu Kwatalo SA
Muhammad Yahaya Jabo
Dr Abdullahi Namadi
Dr Mubarak ES
Dan Majalissar jaha na Kafin Hausa
Dan Majalissar jaha na bulangu da sauran manyan Mutane.

Za'a Gabatar da Taron acikin sakateriya Mulki ta karamar Hukumar Kafin,
Da misalin karfe biyu na Rana,

Muna Rokon Allah ya sa ayi taro lafiya agama,

16/10/2025

SANARWA!!!
Assalamu alaikum warahmatullah.
Don Allah duk ɗalibin dayasan yayi screening na masu gyaran jarrabawar SSCE (NABTEB) daga waɗannan mazaɓun: GAFAYA, RUBA, DA D/TOKA. Su hallara a garin GAFAYA da misalin karfe 12:00 na rana domin suyi THUMBPRINT.

Shamsi Gambo Umar
Chairman Education Development Committee, KUF
16/10/2025.

Gidauniyar SURE 4 U ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Hukumar Shigi da Fici ta Najeriya (Immigration) Rtd CGI Muhamma...
11/10/2025

Gidauniyar SURE 4 U ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Hukumar Shigi da Fici ta Najeriya (Immigration) Rtd CGI Muhammad Babandede OFR,OCM. ta tallafawa iyayen marayu dubu ɗaya da ɗari shida da tamanin da tara (1689) a yankin Hadejia jihar Jigawa.

SURE 4 U ta zaɓo matan 220, iyayen marayu 1689 ne daga ƙananan hukumomi takwas na gundumar Haɗejia jihar Jigawa.

Matan 220 na da yara 1689 a ƙarƙashinsu, waɗanda ɗari bakwai da huɗu (704) ne kacal ke karatu sauran ɗari tara da tamanin da huɗu (984) basu zuwa makaranta.

An bai wa ko wace uwa daga cikin waɗanda aka zaɓo buhun shinkafa mai nauyin 25kg da man gyada da s**ari, da atamfa da kuma Naira dubu Ashirin-ashirin.

Yayin taron, sanata mai wakiltar Jigawa ta Gabas Sanata Abdulhamid Malam Madori ya bai wa iyayen marayun tallafin Naira dubu goma-goma su yi kuɗin mota.

09/10/2025

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

ASSALAMU ALAIKUM WARAH TULLAHI TA'ALA WA BARAKATUHU.

ANA SANAR DA AL'UMMA CEWAR IDAN MUTUM YANADA MAI CUTAR FARFADIYA AGIDANSA KO AGIDANSU KO A UNGUWAR SU KO A GARINSU TO GA DAMA TA SAMU.

KUNGIYAR LIKITOCE TASA A NAIMO MATA MASU WANNAN CUTA ZATAI MUSU AIKI KYAUTA.

ABUN DA AKE BUTA SHINE.

1-SUNAN MARAR LAFIYAR.
2-SUNAN GARIN DA YAKE.
3- ADDRESS MARAR LAFIYAR
4-SAI KUMA LAMBAR WAYAR DA ZA'A IYA SAMUN MARAR LAFIYAR.

IDAN AN HADA WAD'ANNAN ABUBUWA SAI A TURAWA WANNAN LAMBAR WAYAR 08030480571.

KUSANI WANNAN AIKI KYAUTANE KUMA ZA'AZO HAR INDA MARAR LAFIYAR YAKE AI MASA AIKI KYAUTA.

IDAN KANA BUKATAR KARIN BAYANI KA IYA KIRAN WANNAN LAMBAR WAYAR 08030480571.

28/09/2025

SANARWA: 📢📢📢 Ga duk dalibin daya cika form din buƙatar gyaran SSCE da aka kamala sati biyu da s**a wuce, aje Ƙofar gidan Hakimin Kafin Hausa dan duba suna. Sannan Kowa ya zama a kusa kuma cikin shiri domin za'a fara Registration, inda za'a fara da Mazabar Kafin Hausa a wannan Litinin din 29/09/2025.

AKIYAYE: Rijistar Online ce dole kowanne ɗalibi yazo da kansa , wani bazai yiwa wani ba.

Vacotional tranning Flag up ceremony  for 160 Youths from the 11 Wards of  Kafin-Hausa Local govt. Organized by Kafin Ha...
27/09/2025

Vacotional tranning Flag up ceremony for 160 Youths from the 11 Wards of Kafin-Hausa Local govt. Organized by Kafin Hausa Unity Forum.

Address

Kafin Hausa Local Government
Kafin Hausa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kafin Hausa Unity Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kafin Hausa Unity Forum:

Shortcuts

Share

Category