13/10/2026
KU SHIGO TARE DA MU JIRGIN TSIRA (01)
Rubutawa: Dr. Muhammad bn Abdurrahman Al-'Arifi
Fassarawa: Muhammad Ibrahim Bawa Mai Shinkafa Abu A'isha
GABATARWA
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.
Godiya ta tabbata ga Allah, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah ﷺ. Bayan haka:
Na farko:
Wani mutum ya zauna a gabana cikin damuwa da baƙin ciki, sai ya ce:
“Ya Sheikh, na gaji da zaman ƙasashen waje.”
Sai na ce masa:
“In shā Allah, Allah Ya gaggauta dawo da kai wajen iyalanka da garinka.”
Sai ya fashe da kuka, ya ce:
“Wallahi ya Sheikh, da ka san irin kewar da nake yi musu, da kuma irin kewar da suke yi mini!
Shin za ka yarda, ya Sheikh, cewa mahaifiyata ta yi tafiyar fiye da mil ɗari huɗu domin ta je wajen kabarin wani shehi, ta roƙe shi ya mayar da ni gare ta?!
Ai wai shi mutum ne mai albarka; addu'o'i ana karɓa saboda shi; yana yaye damuwa; yana jin addu'ar masu roƙo, har bayan mutuwarsa!”
Na biyu:
Malaminmu, Sheikh Al-'Allāmah Abdullah bn Jibrīn, ya ba ni labari, ya ce:
“Na kasance a filin Arafah. Mutane suna kuka suna addu'a. Sun sanya ihrami, sun ɗaga hannayensu zuwa ga Allah, Sarkin sarakuna.
Yayin da muke cikin ƙasƙantar da kai da ibada, muna neman rahama daga sama,
Sai wani tsoho ya ja hankalina. Ƙashinsa ya raunana, jikinsa ya yi laushi, bayansa ya lanƙwashe. Yana ta cewa:
‘Ya waliyyin Allah wane! Ina roƙonka ka yaye mini damuwata. Ka yi mini ceto. Ka tausaya mini.’
Yana kuka yana rushewa.
Sai jikina ya firgita, fatata ta yi tsikar zakara. Na ce masa:
‘Ka ji tsoron Allah! Ta yaya za ka roƙi wanin Allah? Ta yaya za ka nemi buƙatunka ga wanin Allah? Wannan waliyyin halitta ne kamarka, bawa ne mallakin Allah. Ba ya jin ka, ba ya amsa maka. Ka roƙi Allah Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya.’
Sai ya juyo gare ni ya ce:
‘Ka ƙyale ni, kai tsoho! Ba ka san matsayin wannan shehin a wurin Allah ba! Ni na yi imani ƙwarai cewa babu ko ɗigon ruwa da yake sauka daga sama, kuma babu ƙwayar iri da take tsiro daga ƙasa sai da izinin wannan shehin!’
Da ya faɗi haka sai na ce masa:
‘Subḥānallāh! Me ka bari wa Allah? Ka ji tsoron Allah!’
Da ya ji haka daga gare ni, sai ya juya baya ya tafi.”
Na uku, na huɗu da na biyar, labaransu suna cikin shafukan da ke gabanka.
Subḥānallāh! Ina waɗannan da suke neman mafaka ga wanin Ubangijinsu? Masu neman buƙatunsu a wurin matattu? Masu kai damuwarsu ga ƙasusuwan da s**a lalace da gawawwakin da ba su motsi?
Ina s**a bar Allah, Sarkin gaskiya bayyananne? Wanda Yake ganin motsin jariri a cikin mahaifa, Yake jin addu'ar masu damuwa, kuma ba Ya yarda bayinsa su roƙi waninsa.
Ka yi kuka idan kana so saboda halin da al'umma ta shiga. Ka kalli ƙasashen Musulmi, za ka ga kaburbura, wuraren ibada da ake dangantawa da waliyyai, da ƙabarai da ƙasusuwan matattu sun zama mafaka lokacin bala'i, kuma wurin gudun neman taimako lokacin damuwa.
Ƙarami ya tashi a kan wannan aƙida, babba kuma ya tsufa a kanta.
Waɗannan kalmomi ne gare su; nasihohi ne da tunatarwa; zantuka ne da kiraye-kiraye. A'a, kururuwa ne da gargaɗi; addu'o'i da roƙo ga waɗanda s**a nutse s**a kauce.
Waɗanda raƙuman ruɗani s**a yi ta jefa su, s**a ɓace a cikin hanyoyi.
Har s**a rasa Jirgin Tsira, s**a mutu suna cikin shirka, alhali suna zaton su Musulmi ne.
Lallai wannan shi ne Jirgin Tauhidi, wanda yake kamar Jirgin Annabi Nuhu (A.S.). Duk wanda ya hau shi zai tsira, wanda ya ƙi hawa kuma zai halaka.
Hakika mun ga a ƙasashen Musulmi dangi, 'yan'uwa, maƙwabta da abokai da yawa, waɗanda ayyukansu s**a lalace a rayuwar duniya, alhali suna zaton suna kyautata aiki.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
﴿قُلْ هَلْ نُنَبِّئُكُمْ بِالْأَخْسَرِينَ أَعْمَالًا الَّذِينَ ضَلَّ سَعْيُهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ يَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ يُحْسِنُونَ صُنْعًا﴾
(Suratul Kahf: 103-104).
Saboda haka aka rubuta wannan littafi domin ya zama kira gare su baki ɗaya, su bautawa Allah Shi kaɗai, ba tare da haɗa Shi da wani ba.
Marubuci:
Dr. Muhammad bn Abdurrahman Al-'Arifi
Digirin Digirgir (PhD) a fannin Aƙida da Mazhabobin Zamani.