24/07/2026
βKada ka kuskura ka sake Jin MUSIC (kida) a matsayin abin wasa, ba tare da ka san ainihin hatsarin da kake janyo wa kanka ba.
Ina so in koya muku ilimin Metaphysics, don haka ina buΖatar nutsuwarku.
β
βAbin da mutane da dama ke kiransa da kiΙa, a ilimin Metaphysics wani makamashi ne na frequencies da ke gudanar da sauye-sauye a cikin halittar Ιan adam. Abinda baka sani ba kuwa sauti shi ne kaΙai Ζarfin (energy) da ke iya shiga cikin tunaninka (conscious mind) da gangar jikinka ba tare da ya nemi amincewarka ba.
β
βNi da kai duka bamu da jaa akan wannan idan mukayi tunanin yadda wakar nan ta JARUMA ta Hamisu breaker take samu tunanin wanda mukafi kauna ba tare da mun shirya ba.
β
βA cikin littafin The Secret Doctrine, H.P. Blavatsky ya bayyana cewa sauti shi ne babban makamashin halitta (Cosmic Sound/Nada Brahma), wato wata al'ada ta ciki (internal control) wadda ke iya gina sabuwar Ζaddara ko kuma rushe tsarin laka (spinal cord) da amsawan jijiyoyin ΖwaΖwalwa ba tare da kowa ya lura ba.
A zahirin tarihi da ilimin fassarar harsuna (Etymology), kalmar MUSIC ta fito ne daga harshen Tsohuwar Greek wato Mousike, wanda yake nufin Fannin Muses wato tsarin tsafi ne na Greek, Muses sune aljannun da ke ba mutane basirar wake-wake da fasaha.
β
βIdan ka zurfafa bincike a kan tushen kalmar ME-U-SIC, za ka fahimci wata boyayyar gaskiya ta Metaphysics a cikinta da ke nufin "Me and You Sick" wato lalata tsarin makamashin jiki tsakanina da kai ko kuma Ka iya cewa "Lalata tsarin tunaninka, kai da kwakwalwarka."
β
βMasana philosophy na tarihi irin su Pythagoras sun bayyana cewa kowane sauti yana da nasa tsarin mitoci (Vibrational Geometry). Lokacin da kake sauraron kiΙan da aka tsara shi a cikin mitocin (frequencies) da ke harzuΖa sha'awa, fushi, ko firgici, akwai wasu saΖonnin boye (subliminal messages) suna ratsa kariyarka/garkuwarka ta ciki kai tsaye zuwa cikin ΖwaΖwalwarka ta ciki (subconscious mind) kai tsaye su haifar da emotion ko feeling.
β
βWannan shi ne abin da Hermeticists ke kira da Law of Vibration, ina nufin cewa duk abin da kunnena ke sauraronsa yana sake tsara yadda jinina ke gudanar da saurin bugun zuciyata, yana kullewa ko buΙe cibiyoyin makamashina (Chakras), haka yake da kai.
β
βA lokacin da mutum ya shiga tafarkin farkawa na ruhi (Spiritual Awakening), babban matakin farko shi ne tsarkake kunnuwa daga waΙannan mitocin da ke gurgunta fahimta. Sanannen masanin Metaphysics, Manly P. Hall, a cikin littafinsa The Secret Teachings of All Ages, ya fito fili ya bayyana cewa tsoffin masana ilimin asiri na Masar da Girka suna amfani da sauti domin warkar da mutane ko domin dasa musu bautar tunani ba tare da an Ιaure su da sarΖa ba.
β
βLokacin da kake sauraron kiΙan da ke cike da abubuwan buΖatu na sha'awa ko hargitsi, kana rage kwarjinka ne (Lowering your Vibration), wanda hakan ke kawo mancewa da ainihin yanda kake da kuma toshe hanyoyin buΙewar idonka na uku.
β
βRabuwa da waΙannan frequencies na hargitsi da sake gyara abubuwan da kake sauraro shi ne tushen 'yantar da ruhinka daga bautar zamani. Lokacin da ka tsaftace abin da ke shiga kunnuwanka, jikinka yana komawa zuwa ga tsarin dabi'arsa na asali, tunaninka yana samun nutsuwa da kwarjini, sannan idanunka za su buΙe wajen fahimtar gaskiyar da ake Ιoyewa a bayan wannan maganganun da ake musu sauti.
β
βIdan har kana son kasancewa a tafarkin farkawa da samun haΙin kai da ainihin gaskiya, dole ne ka zama mai zaΙe, mai tsauri a kan waΙanne mitoci kake amfani da su wajen ciyar da ruhinka kowace rana, domin duk abin da ya shiga cikin tunaninka shi ne ke tsara Ζaddararka ta gobe.
β
βPeace and blessings.
β
β
β
β