PEACE BOY TV F.T.A

PEACE BOY TV F.T.A I am here for you, but I will never give up for making you to be happy,thanks you to all my friends

lol 😂 imagine wai dan Allah wane dalili kake dashi ne wai kace kana tsoran mutuwa ko qaddarah lol 😂 wanda kasan duk daga...
17/10/2025

lol 😂 imagine wai dan Allah wane dalili kake dashi ne wai kace kana tsoran mutuwa ko qaddarah lol 😂 wanda kasan duk daga Allah suke mutuwa dai ba fashi dole ko kaso ko kaqiii duk wanda ya mutu lokacin sah yayine kaima kajira nakah babu dabarah
1. ai sojane shiyasah ya mutu
2. ae driver ne shiyasa nake tsoran tuqi
3. ae da. Nepa ne shiya wuta ce takashe shi shi yasa ko kyau bana iya aikinnn
3. ae dan mining ⛏️ ƙasa ce ta danne shi kai koda Banda aiki ba zan iya wann aikin bah aikin mutuwa
4. police ne ɓasayi s**a kashe shi wani ae bazan iya aiki bah wani takasheni abanza
5. ai injin niƙa garai akan bel din injin ya kashe shi
abinda baku fahintah anan shine rai dai dayane duk dubararka da yadda kakai da sanshii Sai yabarkah babu dabarah mutum nawane suke bacci da iyalinsa su farka suga dayan ya mutu mutum nawane saboda jin dadi suna tsaka da cin abinchi zai mutu wanda ko lomar abincin bai haɗiye bah ita duniya ba taragoba ce katashii duk wani tunanin zaka mutu akan aikin da kake sai lokaci yayi duk da kasan wataran zakai ban kwana da duniya kaso ko baka so bah 😐 Allah yasa mudace

Malamin ya shiga cikin aji sai ya tarar da kujerar da yake zama a rataye a saman ajin.Cikin nitsuwa ya kalli Ɗaliban yay...
18/09/2025

Malamin ya shiga cikin aji sai ya tarar da kujerar da yake zama a rataye a saman ajin.

Cikin nitsuwa ya kalli Ɗaliban yayi murmushi.. Ba tare da furta komai ba sai ya nufi allo ya rubuta:

"Test 15 mins, 30 Marks"...

Q1. A nemo nisan dake tsakanin Kujera da kuma floor na ƙasa ta ma'aunin centimeters (1 Mark)

Q2. A nemo angle of inclination na kujerar tsakanin ta ceiling, sannan a nuna yadda akayi aka samo. (1 Mark)

Q3. A rubuta sunan Ɗalibin da ya rataya kujerar a sama da kuma waɗanda s**a taimaka mishi wajen hakan. (28 Marks).

Cikin sauƙi Malamin yayi ram da masu laifin. 😀😀😀.

Copied

Wani Farfesa a fannin ilimin shari'a ya tambayi ɗaya daga cikin dalibansa a cikin aji:“Menene sunanka?”Sai ɗalibin ya ba...
04/09/2025

Wani Farfesa a fannin ilimin shari'a ya tambayi ɗaya daga cikin dalibansa a cikin aji:
“Menene sunanka?”

Sai ɗalibin ya ba shi amsa cikin ladabi da girmamawa, amma nan take malamin ya kore shi daga cikin ajin ba tare da ya ba da wani dalili ba.

Ɗalibin ya yi ƙoƙarin kare kansa, amma malamin ya hane shi magana ya kuma tilasta masa fita daga cikin ɗakin karatun.

Sai ɗalibin ya fita yana jin an zalunce shi, sauran ɗaliban kuma s**a yi shiru.

Daga nan sai malamin ya fara darasi, ya tambayi ɗaliban:
“Me ya sa ake kafa dokoki?”

Wani ɗalibi ya tashi ya ce: “Don a daidaita halayyar mutane.”
Wani ɗalibin kuma ya ce: “Don a tabbatar da an aiwatar da su.”
Wani na uku ya ce: “Don kar mai ƙarfi ya zalunci marar ƙarfi.”

Sai malamin ya ce: “Eh, haka ne, amma har yanzu ban gamsu ba.”

Sai wata ɗaliba ta ɗaga hannu ta ce: “Don adalci ya tabbata a cikin al’umma.”

Sai malamin ya ce: “Eh, wannan itace amsar daidai. Ana kafa dokoki domin adalci ya wanzu a cikin al’umma.”

Sai ya sake tambaya:
“To me ne amfanin adalci?”

Wani ɗalibi ya amsa: “Don a kiyaye haƙƙoƙi, kuma kada a zalunci kowa.”

Sai malamin ya ce:
“Yanzu ku bani amsa ba tare da jin tsoron komai ba. Shin, na zalunci ɗan ajinku lokacin da na kore shi?”

Dukkan ɗaliban s**a ce: “Eh.”

Sai malamin ya ɗaga murya ya ce:
“To me ya sa kuka yi shiru ba ku yi komai ba?!
Me ne amfanin dokoki idan ba mu da haɗin gwiwar tsayawa wajen aiwatar da su?!”

“Idan kuka yi shiru lokacin da aka zalunci wani, ba ku kuma kare gaskiya ba, to kun rasa 'yancinku na ɗan Adamtaka. Sannan kuma ku sani shi 'yanci ɗan Adamtaka ba a siyar da sa.”

A ƙarshe, sai malamin ya kira ɗalibin da ya kora, ya nemi afuwarsa a gaban kowa, ya kuma ce:

“Wannan shi ne darasinku na yau. Kuma ya zama wajibi ku aiwatar da shi a cikin al’umma tun daga yau har zuwa ƙarshen rayuwarku.”

KIRARIN TELOLI Tela sa zare biyu aiki,Tela a baka kudi aga aiki, a hana ka kudi aga lalaci.Tela mai fitar da mutane kuny...
01/09/2025

KIRARIN TELOLI

Tela sa zare biyu aiki,
Tela a baka kudi aga aiki, a hana ka kudi aga lalaci.
Tela mai fitar da mutane kunya.
tela in baku ba kafacity.
tela ba'a kasa ka sai dai ka kasa.
tela mai batawa dannan ya gyara.
tele wajen zamun ku a aljanna ma daban yake.
Tela waliyin Allah mai rufewa dan adam tsiraici.

- Dinki ba kudi ajiya
-Tela a baka kudi aga kyakkyawan aiki aki biyanka aga danyan aiki
-Tela mai fitar da cele kunya
-Tela mai fitar da ango da amarya da iyayensu a kunya
-Tela abokin mai kudi abokin talaka

KAJI NAWA KAI MA MUGA NAKA.

‎MUTUWAR BUHARI ALKHAIRI CE‎-----------------------------------‎‎Ba mutuwar ce tafi daga min hankali ba wallahi, domin n...
16/07/2025

‎MUTUWAR BUHARI ALKHAIRI CE
‎-----------------------------------

‎Ba mutuwar ce tafi daga min hankali ba wallahi, domin na san ta kowa tana tafe. Abun da ya fi damu na shi ne, ya roke mu gafara kafin ya tafi, kuma da yawan mu an yafe masa. Amma mu kuma bamu da damar rokon tashi gafarar akan abun da muma muka yi masa, domin dole akwai.

‎ Ba zamu sake ganin shi ba sai a filin alkiyama, gamu, gashi a gaban ubangiji- zamu maimaita zantukan mu da posts din mu a kan shi na gaskiya da na karya. Lokacin kuma ba a yafiya. Indai wannan bai daga maka hankali ba, ban san kuwa me zai daga shi ba, dan uwa.

‎Hakika mutuwa darasi ce ga mai Imani. Allah ka sa mutuwa ta ci gaba da koya mana kokarin fita hakkin bayin ka kafin mu rasa damar neman yafiyar su. 😭

MashaAllah! Anga Watan Karamar Sallah A Saudiyya. Hakan Na Nufin Gobe Lahadi Ne Ranar Karamar Sallah A Duniya.Allah Yasa...
29/03/2025

MashaAllah! Anga Watan Karamar Sallah A Saudiyya. Hakan Na Nufin Gobe Lahadi Ne Ranar Karamar Sallah A Duniya.

Allah Yasa Mu Dace Amin

28/03/2025
RAMADAN DAY 28ALLAH Kaine ALLAH! ✨💖Ya ALLAH! Kai ne kaɗai Masani, Kai ne kaɗai Mai iko akan komai. Kai ne Mai yanke huku...
28/03/2025

RAMADAN DAY 28

ALLAH Kaine ALLAH! ✨💖

Ya ALLAH! Kai ne kaɗai Masani, Kai ne kaɗai Mai iko akan komai. Kai ne Mai yanke hukunci ba tare da kuskure ba! Kai ne Mai cika buri, Mai amsa addu’o’i, Mai bayar da nasara ga bayinka. 🕊️🤲

Ya ALLAH! Mun dogara gare Ka, mun miƙa rayuwarmu da burikanmu gare Ka. Kai ne Ka san sirrin zukatanmu, Kai ne Ka san damuwar da ke cikin zuciyarmu. Ya ALLAH! Ka cika mana burikanmu na alheri, Ka yi mana jagora a dukkan al’amuranmu. 🤲💫

Alfarma ta Annabi Muhammad ﷺ, Ya ALLAH Ka shafe mana damuwarmu, Ka kawo mana sauƙi a rayuwarmu, Ka cika mana buri na alheri, Ka sa mu rayu cikin farin ciki da albarka. 💕🕊️

Ya ALLAH! Kai Kasan Karatun Kurma, Kai ne Mai Hikima da Adalci. Idan Ka ce "KUN FAYAKUN" sai ya kasance! Yav ALLAH! Ka bamu ikon cin nasara a rayuwarmu, Ka azurta mu da abinda yafi alheri, Ka kare mu daga sharrin duniya da lahira! 🤲✨
Allah Kai mana gafara
Allah kai Mana afuwa
Allah Kai Mana arziki duniya da lahira
Allah Ka yafe Mana
Allah Ka samu cikin yantattu
Allah Ka yaye Mana damuwa
Allah Ka sakawa iyayenmu
Allah Ka biya musu bukatunsu
Allah Ka sakawa malamanmu
Alkah ka Zama gatansu

Allah Mata da Maza ka Basu abokan rayuwa nagari
Allah masu auren ka zaunar dasu lafiya
Allah ka yalwata gidajensu
Allah Ka azurtamu da wadatar zuci,
Allah ka core mana hassada, gulma, giba, Gilli da nufaka.
Allah ya cire mana girman Kai da dagawa
Allah Ka tsaremu mugun ji da mugun gani
Allah kai mana sutura da'iman
Allah ka karemu biyayya gareka
Allah ka hanemu saba maka
Allah ka biya Mana bukatunmu Wanda muka Gaya da Wanda bamu Gaya ba.

Allahumma innaka Afuwwun tuhibbul afwa fa'fu anna🤲

- Ramadan Day 27 🌙❤️🕌
27/03/2025

- Ramadan Day 27 🌙❤️🕌

RAMADAN DAY 26MAI AZUMI KAYI ADDU'A.-"Yana daga cikin ladabin bawa nagari mai azumi shi ne: yawaita yin addu'ar Allah ta...
26/03/2025

RAMADAN DAY 26

MAI AZUMI KAYI ADDU'A.
-
"Yana daga cikin ladabin bawa nagari mai azumi shi ne: yawaita yin addu'ar Allah ta'ala ya karɓi azuminsa, ya sanya shi daga cikin bayin da yake ƴan'tawa a cikin wannan wata mai albarka na ramadana, ya kuma nesanta shi daga cikin gafalallu masu asara. Kada kayi wasa da yin addu'a a rayuwarka musamman a cikin azumin nan, ka roƙi Allah ya gafarta maka, yayi maka albarka"
-
"Kada kayi wasa da addu'a a rayuwarka, musamman a irin wannan lokaci mai tsada da daraja, ya kasance koda yaushe bakinka a cikin yanayi na addu'a da ambaton Allah yake"
-
"Kayi addu'a da kyakkyawan yaƙi da tawassili da azumi ko ibadar da kakeyi, da sannu Allah ta'ala zai amshi dua'inka.

Ramadan day 25Ya Allah continue to lift us above all challenges in life. Never imposed on us that which we have no stren...
25/03/2025

Ramadan day 25

Ya Allah continue to lift us above all challenges in life. Never imposed on us that which we have no strength to bear, grant us mercy, favour & blessings. Grant us good health & let us end with the most beautiful acts in this life , forgive our beloved one's, crown our efforts with success, May Jannatul Fidaus be our final destination

Address

Goya Road
Funtua
9409163597799014

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when PEACE BOY TV F.T.A posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to PEACE BOY TV F.T.A:

Share

Category