12/04/2026
Tun shekaru Dari Huɗu kafin jihadi Hausawa ke zuwa aikin Hajji, Amsar tambayar "yaya Ingancin Musulunci a Kasar Hausa Kafin tawayen Jihadi"?
Da yawa ba su san cewa kafin a kai ga tawayen jihadi akwai wani lokaci mai suna “Hausaland Islamic Golden Era” wani zamani da mafi yawan sarakunan Hausa manyan malamai ne, kuma Musulunci ya yi karfi ya bazu a lungu da saƙo. Tun shekaru 500 kafin jihadin.
A Zazzau, Sarki sheikh Muhammad Makau fitaccen malami ne, ɗan Tititibirin malami Isyaka Jatau.
A Kano, Sarki sultan Muhammad Alwali babban mahaddacin Al-Kur’ani ne.
A Katsina kuwa, Sarki Sultan Magajin Haladu, jikan Sarki Korau, ya shahara da ilimi.
A Gobir, Sarki sultan Muhammad Yunfa ya rubuta Al-Kur’ani da hannunsa, wanda har yanzu yana nan a gidan tarihi a kaduna.
A Daura ma akwai Sarki Sultan Abdullihi Tsoho (Audu Tsoho), wanda ya shahara da hakuri da bin tsarin Musulunci.
Dukkanin waɗannan sarakuna suna gudanar da tsantsar shari’ar Musulunci, ana zaune lafiya, kuma addinin ya karfafa sosai. Katsina ta zama cibiyar ilimin addini ta biyu a yammacin Afirka bayan Timbuktu.
A yawan lokuta ana faɗa cewa hanya ɗaya ce Musulunci ya shigo:
ta hannun Larabawa masu zuwa fatauci.
Amma akwai wasu hanya da ba a so ku sani .
1. ta hannun Hausawa da s**an tafi kasar Larabawa yin fatauci, s**a karɓo ilimi da addini s**a dawo da shi gida.
Farfesa Bunza ya bayyana cewa:
“Babu wanda zai iya cewa ga tak**aiman lokacin da Musulunci ya fara shigowa kasar Hausa. Sai dai kimantawa.”
Musulunci dai ya shafe fiye da shekaru dubu 1200 da fara bunkasa a kasar Hausa. Kafin ya zama addinin gwamnati, akwai dubban malamai da dalibai.
Sarakunan gargajiya sun ba da ‘yancin addini yadda ya k**ata — har ma suna da wakilan Musulmi a cikin fada tun kafin sarakuna su karɓi Musulunci gaba ɗaya.
Misali: kafin Sarki Muhammad Korau ya zama Sarkin Musulmi na farko a Katsina, tuni akwai Alkalai a fadar Sarki Sanau, wanda shi ba Musulmi ba ne. Wannan ya faru fiye da shekaru 700 da s**a shuɗe.
Tarihi da Tatsuniyar Bayajidda
Koda labarin Bayajidda tatsuniya ce, akwai abubuwan lura bayajidda musulmi ne, me suna ummaru.
Kena jikokin Bayajidda – Bagauda da Bawo Musulmai ne, hakan na iya nufin cewa tun a karni na 9 an fara samun sarakunan Musulmi a Kano da Katsina da Gobir da Zazzau da Rano.
Hallau akwai shaidu cewa tun sama da shekaru 400 Hausawa ke zuwa aikin hajji. Wannan ya sa a yau ake samun Hausawa fiye da miliyan 10 a Sudan, wasu kakanninsu sun tsaya ne bayan hajj, wasu kuma saboda kasuwanci.
Daya daga cikin manyan malamai Hausawa shi ne Al-Shaykh Yūnus Ɗan Muhammad al-Ḥawsawī Al-Kānawī,
wanda ya yi fice a ilimin Musulunci tun a karni na 18. Ya yi doguwar tafiya daga Kano zuwa Makka neman ilimi (1728–1731 M).
Part 1.
NB: shi wannan hoton ba shi da alaka da post din, hoton wani bahaushe ne, ya yi mani kyau ne kawai.
Ibrahim Gamji.