Arewa Business Hub

Arewa Business Hub Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa Business Hub, Financial service, Kano.

Empowering Northern Entrepreneurs to grow smarter online 🚀
Digital Marketing • Business Coaching • Social Media Management
DM me for business strategy & growth consulting đź“©

Inde kai matshi mai ka kai 25 to 30 years wannan zai taimake ka Babu wani mahaluki da ya fi shiga matsin lamba da ƙuncin...
25/05/2026

Inde kai matshi mai ka kai 25 to 30 years wannan zai taimake ka

Babu wani mahaluki da ya fi shiga matsin lamba da ƙuncin zuciya, irin matashin da yake tsakanin shekaru 25 zuwa 32 wanda yake jin kamar lokaci yana ƙure masa.

​Wannan shine lokacin da kuruciya take ƙarewa, nauyin zama cikakken namiji kuma ya hau kanka gadan-gadan. Idan ka duba gefe, za ka ga sa'anninka suna sayen filaye ko gina gidaje. Idan ka duba wani gefen, za ka ga wasu suna auren matan da suke so. Idan ka kalli kanka... sai ka ga har yanzu kana fafutukar ganin ka tsira da kudin abincin gobe ne kawai

​Wannan lissafin shine yake hana ka barcin dare.

​Yana sa ka ji tsoron cewa iyayenka suna tsufa, alhali baka fara yi musu hidimar da ka dauki alwashin yi ba.
Yana sa ka ji tsoron tunkarar macen da kake so don gudun wulakancin rashin abin hannu.
Yana sa ka ji kamar ka gaza a rayuwa, ko kuma kamar ka makara an bar ka a baya.

​Tsananin tunanin yadda za ka warware wannan kuncin, shi yake sa ka janye jikinka daga mutane, ka koma kai kadai kana magana a zuciya. Ka zama mai yawan shiru.

​Amma dan uwana, ina so ka numfasa ka natsu.
​Ba lokaci ne yake kure maka ba. Wannan matakin da kake ciki, shine ainihin wutar da take gasa kowane d'a namiji kafin ya zama karfe. Kasancewar kana jin wannan damuwar a ranka, ya nuna cewa kai namijin kirki ne mai kishin goben sa, ba wanda ya zubar da makamansa ba.

​Tsarin kaddarar wani, ba zai taba zama naka ba. Agogon kowa da irin lokacin da yake bugawa.
​Ka daina auna nasararka da ta wasu. Ci gaba da zubar da gumi a hankali, ci gaba da hakuri komai za dadaita in sha Allah...

​Arewa Business Hub

Kuskure mafi girma da zaka aikata a matsayinka na dan kasuwan mai kokarin tara jari...​Shine ka fara yin rayuwar masu ku...
24/05/2026

Kuskure mafi girma da zaka aikata a matsayinka na dan kasuwan mai kokarin tara jari...

​Shine ka fara yin rayuwar masu kudi a lokacin da kake matakin neman kudi. Wannan ita ce asalin gubar da take kashe kasuwancin mutane. Idan har kana son tara jarin da zai baka 'yanci, ka guji wadannan manyan kurakuran:

1.​Cinye Irin Shuka: Ka samu riba kadan a kasuwa, maimakon ka mayar ka kara girman jarin, sai ka tafi ka sayo abubuwa marasa amfani don ka nuna wa duniya ka fara samun kudi. Wanda ya cinye irinsa a lokacin damina, zai mutu da yunwa a lokacin rani.

2. ​Karyar "Zan Maida": Ka dauki kudin kasuwanci ka biya wata bukata ta kashin kanka ko ta gida, kana yi wa kanka alkawarin "Idan na samu zan maida." Wannan ita ce satar da tafi kowace sata muni, domin kanka kake wa fashi da makami.

3. ​Hada Asusun Aljihu da na Kasuwa: Matukar baka raba kudin da kake ci da kudin da kasuwancin yake bukata ba... zaka wayi gari ka cinye shagon gaba daya kana tunanin riba kake ci.

4. ​Tausayin Banza: Ka dauki kudin jari ka bayar da bashi ga aboki ko dan uwa da sunan kunyar zumunci, alhali kasan ba zasu biya ba. Kasuwanci bashi da dangi, idan ka hada kasuwanci da jin kunya, zaka koma neman na abinci.

5. ​Gasa da Masu Kudi: Kana kokarin yin shigar da masu kudin da s**a kwashe shekaru 10 suna gina daularsu suke yi, alhali kai kana watan ka na shida.

​kudi basa zama a wajen wanda baya mutunta su.
idan kana neman Capacity na karya a waje, zaka samu talaucin gaske a daki.

​Burhan Smart Trade

HANYA ĆŠAYA DA ZAKA FARA CANZA RAYUWARKA YANZU:A cikin rayuwa, sau da yawa muna samun kanmu muna jira. Muna jiran mu sami...
01/01/2026

HANYA ĆŠAYA DA ZAKA FARA CANZA RAYUWARKA YANZU:

A cikin rayuwa, sau da yawa muna samun kanmu muna jira. Muna jiran mu sami isasshen kuÉ—i, muna jiran mu kammala karatu, muna jiran mu sami aiki. Muna tunanin cewa canji mai girma yana farawa ne da wani abu mai girma. Wannan tunani yana da matukar haÉ—ari musammanga matashi, domin gaskiya ita ce, mafi girman lokacin da za ka fara canza rayuwarka shine yanzu, Kada ka bari yini É—aya ya wuce ba tare da ka É—auki mataki ba.

Manzon Allah (SAW) ya taɓa cewa, “Idan mutum ya dogara ga Allah da gaske, zai wadace shi.” Amma kuma, dole ne ka fara da aikin hannunka. Ba za ka iya jira ba tare da ka yi wani abu ba, kace ai komai na Allah ne, Ka fara ko da da ƙaramin abu nw, kuma ka yi imani da cewa Allah zai buɗe maka hanyoyi da yawa. Idan kana so ka gina kasuwanci, ka fara da sayar da wani abu mai sauƙi. Duk wani abu da kake so ka fara shi ko da da kadan ne, ka fara da abin da ka iya sannan ka fara da abun da yake hannun ka.

Ka tuna, mafi girman abin da zai iya hana ka ci gaba shine tsoron faÉ—uwa. Amma a cikin faÉ—uwa ne ake koyo. Kada ka ji tsoron yin kuskure, domin kowane kuskure darasi ne. Yi wa kanka alkawarin cewa za ka tashi tsaye duk lokacin da ka faÉ—i, kuma za ka ci gaba da tafiya. Fara yanzu, kuma za ka gani, rayuwarka za ta canza in sha Allah.
By CEO AREWA DIGITAL HUB
BURHAN.📝

Barka da sabuwar shekara ta 2026 Masu daraja mambobin Arewa Business Hub muna yi muku fatan alheri nasara da cigaba a wa...
01/01/2026

Barka da sabuwar shekara ta 2026

Masu daraja mambobin Arewa Business Hub muna yi muku fatan alheri nasara da cigaba a wannan sabuwar shekara Allah Ya sa 2026 ta zama shekara ta samun riba, ilimi mai amfani, damar kasuwanci da bunkasar dukkan ayyukanmu.
Muna godiya sosai da kasancewarku tare da mu. Ku ci gaba da kasancewa da mu domin muna zuwa da sabbin dabaru, horo, shawarwari da damar da za su daga kasuwancinku zuwa mataki na gaba in sha Allah.
Shekara mai albarka, Arewa Business Hub

Assalamu alaikum abokanmu na Arewa Business HubMun kwana biyu ba mu yi posting ba saboda muna diba sabbin dalibai da s**...
16/12/2025

Assalamu alaikum abokanmu na Arewa Business Hub

Mun kwana biyu ba mu yi posting ba saboda muna diba sabbin dalibai da s**a shiga shirinmu na consulting, coaching, da mentorship na ta karatu.

Amma yanzu muna farin cikin sanar da ku cewa Arewa Business Hub zamu dawo da sabbin updates, tips da darussa masu amfani a page dinmu

Ku tabbata kun kasance tare da mu don samun sabbin labarai, shawarwari, da damar ci gaban kasuwanci.

âś… Ku like, ku follow, kuma ku raba wannan post din don kowa ya samu labarin dawowarmu

Assalamu alaikum ina yi maka godiya sosai bisa amincewa da Arewa Business Hub wannan shi ne onboarding dinmu 👇👇👇👇1. Cika...
11/12/2025

Assalamu alaikum ina yi maka godiya sosai bisa amincewa da Arewa Business Hub wannan shi ne onboarding dinmu 👇👇👇👇

1. Cikakken Tattaunawa (Consultation):
Zan fara tattara duk bayanan kasuwancin da kake so a gyara ko ka fara za mu tantance matsaloli, dama, da yuwuwar ribar ka.

2. Tsara Strategy:
Zan rubuta maka cikakkiyar business strategy da stepstofollow domin ka samu sakamako cikin gaggawa.

3. Mentorship:
Zan kasance tare da kai a mataki mataki ina koya maka dabaru, gyara kuskure, da ba ka shawarwari masu amfani.

Idan akwai bayanai ko abubuwan da kake so na fara da su, ka sanar dani yanzu.
Arewa Business Hub muna godiya sosai🙏🙏🙏

Assalamu alaikumNagode sosai kwarai da yadda ka biya rabin kudin aikin wannan alamar amana ce da girmamawa daka nuna min...
11/12/2025

Assalamu alaikum
Nagode sosai kwarai da yadda ka biya rabin kudin aikin wannan alamar amana ce da girmamawa daka nuna min

Insha Allah zan fara aikin da cikakkiyar kulawa da kwarewa domin ka samu sakamakon da ya fi tsammaninka.

Idan akwai wani karin bayani ko karkata da kake so mu saka a cikin aikin ka sanar dani.

Nagode da yarda da Arewa Business Hub.

Duk wanda bashi a wannan Class VIP to wlh anayi babu kai bro/ sisterOpration Smart Money Bath 2& 3 Special VIP Program f...
10/12/2025

Duk wanda bashi a wannan Class VIP to wlh anayi babu kai bro/ sister

Opration Smart Money Bath 2& 3 Special VIP Program for business owners

Inde kina online business kuma kina son kana son samun ciniki kuma baka a wannan class din wlh anayi babu kai bro/sister

Wannan aji shine aji na musamman da muke koyar da yan kasuwa yadda zasu samu ciniki a online business cikin tsari wato strategy na zamanida da innovation na zamani wanda manyan yan kasuwa suke amfani dashi wajen samun ciniki da gwagwgwabar riba

Idan kana son sgiga zaka iya mana magana ta Whatsapp 07067500697 ko ka duba comment zaka ga link da za kai mana magana kai tsaye

DAGA NAKU CEO AREWA BUSINESS HUB BURHAN DIGITAL MARKETER

Address

Kano
700101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Business Hub posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share