11/03/2024
*CIRE TSORO A TRADING DA HAUSA*
Shi Tsoro ajinin Dan Adam yake Kuma kowa da inda tsoron sa yake bayyana amma shi tsoro a kasuwa daban yake sbd wannan kudi zaka rasa kuma babu Wanda idan yasan zai rasa kudi bazaiji tsoro ba sbd kudin kake nema Kuma zaka rasa shi ace bazakaji tsoro ba saidai ita asara a kasuwan ci dole ce kawai abinda zaka saka a ranka shine kayi lissafin abinda idan ka rasa bazaka damu sosai ba sbd kana da hope din cewar wata Rana zaka samu ribar da tafi wannan asarar da kayi a baya.
Misali:-Mu dauki Sojoji a filin yaki munsan Sojoji a filin yaki suna tafiya ne da yaki ni guda 2 Koh dai su dawo a raya koh Kuma a kawo gawar su gida Kuma munsan bawai tsoron mutuwar ne basayi ba sbd Tsoron mutuwar ne ma suke neman dabarin yaki Dan yakar Abokan gabar su kada su cimmusu meyasa basa shakkar shiga filin yaki domin neman kashe Abokan gabar su sbd suna da dabarun yaki da Kuma makaman yaki Amma duk da wadannan abubuwan dasuke dashi baya hana Abokan gabar su su farmake su wani lokacin harsu cimmusu tunda Suma dai a shirye suke kamar yadda sojojin Nan suke a shirye Haka Abokan gaban nasu suke a shirye.
Dalilin rashin tsoron su gurin shiga daji Abu ne guda biyu.
1.Suna da dabarun yaki Wanda S**a kware akai.
2.Suna da makamai Wanda zai Basu damar farmakar Abokan gabar Nan nasu.
Toh kaima trader irin wadannan tunanin na Sojoji dashi zakana shiga kasuwa kaima kana da naka dabarun sbd rasa kudi Babu dadi Amma dole ayi asara a kasuwanci baa son dai asarar tafi ribar yawa.
Abubuwa guda biyun Nan da Sojoji suke hope dasu na shiga daji yaki a gurin trader sune Kamar:-
1.Kai dabarun ka da gogewar ka shine:-Kasan makamarka a kasuwa sannan yazama na kana da Strategy Wanda zakana shiga kasuwar ka dashi.
2.Makamin ka a matsayin ka na trader shine Kasan abinda zaka iya sakawa a matsayin kasadar ka Wanda zaka iya dauka (Risk Management).
Toh indai kasan wadannan abubuwan toh Babu yadda zakayi ganganci shiga kasuwa bakasan yadda zaka iya daukar kasadar ka ba(Proper Risk Management) kasaka abinda zaka iya dauka Koh da ka rasa sa.
✍ICT_Wisdom