18/01/2026
ME YA SAME MU A AREWA? INA MATSALAR TAKE?
Cikin kwana biyu kaÉ—ai labarai daga Arewa sun isa su girgiza zuciyar duk mai hankali:
A Dorayi Chiranchi, Kano, wasu mutane sun shiga gidan wata mata, s**a kashe ta tare da ’ya’yanta 6 zuwa 7.
A Rijiyar Lemo, Kano State, an tsinci gawar jariri, an ƙone shi an jefar da shi a bola.
A Katsina, wani ya rasa ransa saboda cacar baki kan canjin naira É—ari.
A Gombe, wani ya cakawa uban gidansa almakashi saboda ya k**a su sunyi masa sata a shago ya Koresu a shagon, cacar baki ta rikide zuwa kisa.
Tambaya ita ce:
Ina matsalar take? Laifin waye?
âť“ Gwamnati?
Domin gazawar tsaro, talauci, rashin adalci, da rashin tsayayyen hukunci.
âť“ Hukuma?
Domin sakaci, jinkiri, da barin laifi ya zama ruwan dare ba tare da hukunci mai tsauri ba.
âť“ Iyaye?
Domin tarbiyar yara ta lalace, an bar tarbiyya, an bar tsoron Allah, an maye gurbinsa da tashin hankali.
❓ Ko Al’umma?
Domin mun yi shiru. Mun saba da jin labaran zubar da jini. Mun daina tsawatarwa. Mun daina cewa “wannan ba daidai ba ne.”
Gaskiya É—aya ce:
👉 Duka muna da hannu.
Idan ba da aikatawa ba, to da shiru.
Idan ba da shiru ba, to da halatta mugunta ta hanyar rashin tunkarar ta.
Wannan pah duk bayan kidnappers da Boko haram sum suke faruwa.
Arewa na zubar da jini k**ar babu gobe.
Rayuwar É—an Adam ta zama ba ta da daraja.
Kuma idan muka ci gaba da yin shiru, gobe ba za ta tausaya mana ba.
Allah ya kiyaye Arewa.
Allah ya gyara mu.
Allah ya hana wannan bala’i ci gaba.