19/09/2022
ƊAN KIRIFTO A MATAKIN FARKO
Da farko dai kamar yanda aka sani wannan wani darasi ne da naga ya kamata ya ƙirƙiro so domin amfanuwar al'ummar mu na arewacin Nijeriya da wannan ilimi na kirifto(crypto currency).
Kamar yanda na sha fada a baya,idan Allah (se)ya azurtaka da wani ilimi bai kamata ka ɓoye kai kaɗai ba.Kamata yayi ace ka fito da shi duniya ta amfana,hakan ne zai sa a samu cigaba a cikin al'ummar mu da muke fatan samu a kodayaushe.
Duk da nima har yanzu ɗalibi ne mai neman ilimin wannan harka tamu ta kirifto (crypto),amma hakan bazai hana na bada yawa gudummawar ba,kamar yanda sauran mentors namu suke yi,Kamar irinsu Muhd Dandishe Crypto oga Sunusi,Adam Muhammad Mukhtar oga muhammad sheka,da sauransu dai dama,da kuma abokina Nazieer Crypto.wannan dalilin ne yasa naga nima daga cikin abinda Allah ya h**e min na ilimin wannan harka zan fito waɗansu abubuwa da nake ganin ya kamata,wanda yake so ya fara harkar nan yayi domin samun sauƙin fahimtar ta da kuma samun mutuwa a cikinta.
Insha Allah kamar yanda na yiwa wannan darasi laƙabi da DAN KIRIFTO A MATAKIN FARKO.Zan kawo abinda ya kamata ace a matsayin ka na wanda kake so ka fara wannan harka ka sansu a matakin farko kafin ka fara komai.
Ina rokon Allah abinda zamu tattauna ya zame mana mai amfani da dukkanin mu,anan gidan duniya da lahira Ameen.
Nagode
✍️Nasiru Aliyu Abubakar
18/09/2022
05:30pm