28/11/2025
MUZU--MUZU KO LAGE--LAGE
Mus Ojo Lokacin da ka samu dama a baya baka tuna da talaka ba, baka duba inda matsala take ba, baka taimaka wa wanda babu ba. An baka damar raba Offer, amma sai ka tattara ka mika wa 'ya 'yan masu kudi da na kusa da kai. Talaka sai kallo. Matasanmu sai ciwo da fargaba. Aiki kuwa sai ka kasance da suna ko da kuɗi.
Musa Munyi tsammanin mu 'ya 'yan talakawa zamu mora amma abin takaici sai ka dauki 'ya 'yan manya, ka qarawa masu qarfi qarfi sai ka manta da ɗan talaka dan makaranta dan bashi da gata.
Yanzu kuma da lokacin biyan buqatar ka, ta taso kanaso kayi takara a siyasa ka zo, kana son fito da murmushin ka da magana mai sanyi. Amma mu muna da ƙwaƙwalwa, muna da hankali, babu abinda zaisa muyi tare da wanda baya kaunar mu.
Wannan layin bamayi bamu da ikon kowa, amma muna da kishin al,ummar mu wanda bai tuna da mu lokacin daya samu dama ba, bazai tuna damuba, bayan yaci zaɓe ba
Mu tashi tsaye mu kare muradin talakawa lokaci yawuce da za,a yaudaremu da kalmomi masu sanyi gaskiya ce kawai zata ceto mu.
Bamayi domin siyasa ba wasa ba ce.
Bamayi domin talaka ma dan kasa ne, ba ɗan kallo ba ne.
Bamayi domin wanda bai riqe ma amana a cikin duhu ba kada ka bashi amana da safe.
Wannan fitar farko ce ajira rubutuna na gaba.
Isah Aliyu Iseeh✍️