26/08/2023
Ilimin kimiyya, fasaha, kirkira, zurfin tunani an ce sai ka koyi turanci. Gwamnati ma da turanci ta ke cutarka. Karin magana, hikimar zance, adabi wai sai ka ware rana daya tak domin tuni da su, abunda ya kamata a ce da su ka ke amfani kullum. Mutum idan ba turanci ya yi ba, sai ka ringa mishi kallon wanda bai waye ba ko mara ilimi. Ka zo ka na ihu ”ranar Hausa”, to ai saboda yadda aka kwace maka ‘yancinka har ka ke bikin “independence”, haka aka rage wa harshen Hausa muhimmanci shiyasa ka ware rana ka zo ka na borin kunya wai kai ranar tunawa da muhimmancin Hausa.
Idan Hausa na da muhimmanci a wajenka, ba rana za ka ware mata ba. Gwagwarmaya za ka yi ka kwato mata ‘yancinta ta yadda za ta zama harshen karatu a duka makarantu, da harshen gwamnati, da harshen kimiyya, fasaha, kirkire-kirkiren zamani da zurfin tunani. Wannan gwagwarmaya ba na rana daya ba ne. Na duk rayuwa ne.
Ga litattafan da na rubuta da harshen Hausa, a cikin su guda nawa ka karanta?
1. AHMAD DA AISHA
2. DAN KASA A TURAI
3. IKE DA BABAN MAIRO
4. SADIYA DA MALLAM TANKO
5. KHADIJA ‘YAR SHUGABAN KASA DA USMAN DAN KAROTA
6. IYA ‘YAR KAZA
7. DAJIN DAWAKI
A karshe zan bar ku da wannan:
“Rashin kula da Lami a gidansu ne ya sa duk ranar da a ka ba ta tsokar nama, sai an yi shela a gaya wa ragowar ‘yan gidan da makota”.
Written by Bello Habeeb Galadanchi