02/05/2020
LABARI MAI RATSA ZUCIYA
Wata rana a makaranta malamin
koyar da sanin halayyar dan Adam
(Psychology), ya shiga aji yace "yau
zamu yi wani wasa
Malam yace a cikinku wa zai fito
gaban allo a fara da Shi ? Sai wata
daliba Salma ta fito. Sai mlm yace
ta dauki alli (chalk) ta rubuta sunan
mutane 30 masu muhimmanci a
rayuwarta. Salma ta rubuta dangi,
kawaye, abokan karatu da
makwaftanta.
Sai mlm yace ta goge 3 wadanda
basu da muhimmanci sosai a
wajenta. Salma ta goge suna 3 na
abokan karatunta. Sai mlm yace ta
kara goge 5 marasa muhimmanci,
Salma ta goge makwaftanta.
Malam yayi ta umartarta tana
gogewa har sai da ya rage sunaye
4 kadai sune :- Babarta, Babanta,
Mijinta da Danta 1 data haifa. Gaba
dayan dalibai sai s**a nutsu sun
gane cewa wannan ba wasa bane
kamar yanda Malam ya fada da
farko, yazo musu ne da wani darasi
mai muhimmanci.
Sai mlm ya kalli Salma yace ta kara
goge 2 daga sunayen nan da s**a
rage, wannan zabin fa yana da
wuya, Salma tayi jimmm !
Hannunta yana rawa ba'a son ranta
ba idonta ya cika da kwalla ta goge
sunan Babarta da Babanta.
Sai mlm yace ta kara goge 1 Sai
Salma tasaka kuka ta goge sunan
Danta 1 tilo. Sai mlm yace ta koma
wajenta ta zauna. Bayan wani Dan
lokaci sai mlm yayi tambaya, yace
:- " me yasa ta bar mijinta" ?
Iyayefa sune s**a kawo ki duniya
s**a raine ki har kika girma. Danki
kuma ke kika yi cikinsa kika sha
wahalar laulayin cikin kika haife
shi, kika raine Shi, kuma da iyaye
da Da bazaki iya sake wadansu ba,
amma miji ko yaushe zaki iya
chanja wani.
Aji akayi shiru ana jiran amsar
Salma.
Salma cikin nutsuwa da sanyin
murya tace :- "Wata rana iyayena
ina tare dasu s**a dauke ni s**a
kaini gidan miji, idan na kawo
musu ziyara sai su tambayeni,
"lafiya" ? Idan yayi min laifi na taho
gida sai su kira Shi suyi ta bashi
hakuri, s**e na tashi na koma
gidansa". Dana kuma wata rana zai
barni idan ya girma ya mai da
hankali kan sana'arsa da hidimar
iyalinsa. Mutum 1 wanda zai kare
rayuwarsa tare da ni shine MIJINA,
kuma...... Kafin ta kara magana sai
dalibai s**a dauki tafi gaba daya
saboda ta fadin gaskiyar yanda
rayuwa take.
Aure Ba Abin Wasa Bane
Ina Rokon Allah Ya Bamu Mata Na
Gari
Mata Kuma Ka Basu Mazaje Na Gari,. Ameen