King of ajeeboters

King of ajeeboters “📖 Every story is a crown, and I wear them all.”

04/01/2026
04/01/2026

Celebrating my 4th year on Facebook. Thank you for your continuing support. I could never have made it without you. 🙏🤗🎉

02/12/2025

DONE DEAL🫱🏻‍🫲🏽✅
Aure Lokacine Gwauronci Kuma Yanzu Muka Fara
DONE DEAL ✅

“Do not speak unless your words are more beautiful than silence.”— Imam Ali (A.S)
02/12/2025

“Do not speak unless your words are more beautiful than silence.”

— Imam Ali (A.S)

Da dumi'dumi: Sowore Ya Fallasa: “Ba Badaru Ya Yi Murabus bisa kansa Ba  An Kore Shi Ne Don A Buɗe Hanya Ga Janar Christ...
02/12/2025

Da dumi'dumi: Sowore Ya Fallasa: “Ba Badaru Ya Yi Murabus bisa kansa Ba An Kore Shi Ne Don A Buɗe Hanya Ga Janar Christopher Musa!”

Shugaban Sahara Reporters, kuma ɗan gwagwarmayar demokuraɗiyya, Omoyele Sowore, ya tayar da kura a Facebook bayan ya bayyana cewa Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar ba shi da hannu a murabus ɗin da aka sanar — an umarce shi ne ya matsa gefe domin a bai wa tsohon CDS, Janar Christopher Musa, damar shiga kujerar minista.

Sowore ya ce akwai cikakkiyar hujja da ke nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yanke wannan shawara ne sakamakon rashin gamsuwa da halin da tsaron ƙasa ke ciki, tare da niyyar sake fasalin ma’aikatar gaba ɗaya.

Baya ga haka, Sowore ya kuma jawo hankalin jama’a kan sabon matsin lamba daga gwamnatin Amurka, ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Donald Trump, wanda ya nuna damuwa game da yadda ake gudanar da musayar bayanan sirri tsakanin Najeriya da Amurka.

A cewar majiyar da Sowore ya ambata, ana kuma tsananin duba rawar karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, musamman kan zarge-zargen alaƙarsa da rukunan ’yan bindiga a Zamfara, lamarin da ke janyo damuwa a matakin tsaro na duniya.
Sowore ya ce “duk abin da ake boye zai fito fili nan ba da jimawa ba.”

Yayin da gwamnati ba ta fitar da cikakken martani ba tukuna, wannan sabon bayani da Sowore ya zartar ya sanya idanu sun koma fadar gwamnati — domin irin waɗannan tuhumce-tuhumce kan iya jawo sauye-sauye masu zurfi a tsarukan tsaro na ƙasar.

Shugaba Tinubu Ya Yi Matukar Kaduwa Da Rasuwar Sheikh Dahiru BauchiShugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matuƙar alhini ...
27/11/2025

Shugaba Tinubu Ya Yi Matukar Kaduwa Da Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matuƙar alhini kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis yana da shekaru 101.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu ya ce rasuwar Sheikh Dahiru babban rashi ne ba kawai ga iyalai da mabiyansa ba, har ma ga ƙasar gaba ɗaya, yana mai jaddada cewa marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen shiryar da al’umma zuwa ga tafarkin gaskiya.

Shugaban ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran Darikar Tijjaniyya da ya yi fice wajen karantarwa da kuma yaɗa zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Ya ce: “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, kuma muryar da ke kira da hikima da natsuwa. A matsayin fitaccen mai tafsirin Alƙur’ani, ya kasance ginshiƙi wajen ƙarfafa zaman lafiya da tsoron Allah. Mutuwarsa ta bar gibi mai faɗi a wannan fage.”

Shugaba Tinubu ya kuma tuna da addu’o’i da goyon bayan da Sheikh Dahiru ya ba shi a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.

Shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, mabiyansa da dukkan al’ummar Musulmi a cikin ƙasar da waje. Ya roƙe su da su ci gaba da ɗaukaka sunan marigayin ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, kyautata zamantakewa da ƙarfafa kusanci da Allah.

10/09/2025

I got over 10 reactions on one of my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

10/09/2025

Take the cemara make I go Viral Tv $

Address

Adamawa
640001

Telephone

+2348148950744

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when King of ajeeboters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to King of ajeeboters:

Share